Isa ga babban shafi
Italiya

Labarin wasu bakin haure ya girgiza kasar Italia

Yayin da nahiyar Turai ke ci gaba da lalubo hanyar magance matsalar baki da ke kwararar yankin dan samun mafaka, labarin wasu bakin ya girgiza 'yan kasar Italia inda suke ta mahawara a kai.

Reuters/Antonino Condorelli
Talla

'Yan Sanda sun bayyana cewar wani dan kadsar Cote d’Ivoire ne daga cikin bakin ya fita daga sansanin da ake a jiye su, ya kuma dawo da wayar salula, komfuta da na’urar daukar hoto, abinda ya sa jami’ai suka tuhume shi inda ya samu.

Sai ya ce a gindin bishiya ya sa mu, amma bincike ya gano cewar an hallaka mai kayan ne Vicenzo Solano dan shekaru 68, yayin da matar sa ta fado daga gidan sama ita ma ta mutu.

Wannan ya sa shugaban jam’iyyar National league kiran rufe sansanin, amma nan take Firayi Minista Matteo Renzi ya yi watsi da kiran.

Shi kuwa mutumin na biyu Anatoliy Korol, dan kasar Ukraine, wanda ya kwahse shekaru 10 yana zama a kasar, tarar aradu ya yi da ka, wajen hana fashin amma kuma 'yan fashin suka harbe shi a gaban 'yar sa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.