Isa ga babban shafi
Jamus

Jamus ta bukaci Ministoci su taimakawa Yan gudun hijira

Ministan harkokin cikin gidan kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya yi kira ga takwarorinsa na kungiyar kasashen Turai da su bar yin inda inda dangane warware matsalar ‘Yan ci-rani dake tagayara a yankin, yayin da a yau juma’a ‘Yan ci-rani akalla dubu biyu suka soma takawa da kafansu zuwa kasashen Jamus da Austria.

Wasu daga cikin Yan gudun hijira dake neman mafaka a kasashen Turai.
Wasu daga cikin Yan gudun hijira dake neman mafaka a kasashen Turai. REUTERS/Ognen Teofilovski
Talla

Mr. Steeinmeier ya yi wannan kiran ne a yau juma’a a yayin taron ministocin kungiyar Tarrayar Turai a birnin Luxemburg.

Mr. Steinmeier ya ce ba yadda zasu iya warware matsalar dubban ‘yan ciranin muddun aka cigaba da nuna son rai.

Kana ya kara da cewa idan har kungiyar Tarayyar Turai ta samu nasarar cimma matsaya kan warware matsalar bashin kasar Girka, to ashe kalubalen dake gabanta na magance matsalar dubban yan ci-rani, abu ne da yakamata ta duba da kyau ta kuma magance shi da wuri.

A bangare guda, Ministan ya bukaci kasashen Turai da su gaggauta karbar yan ci-ranin da suke cikin tsaka mai wuya yayin da Kasar Hungary ta hana dubban yan ci-rani mafaka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.