Isa ga babban shafi
Jamus-Fafaroma

Fafaroma ya nemi Kiristoci su karbi 'yan gudun hijira a majami'un Turai

Yau Lahadi Fafaroma Francis yayi kira ga daukacin ikilisiyoyin darikar Katolikaon a nahiyar Turai, su dauki dawainiyar iyalai guda na ‘yan gudun, inda yace fadarsa Vatican zata fara wannan karamcin don sauran su bi.

Bakin haure da suka isa kasar Jamus
Bakin haure da suka isa kasar Jamus REUTERS/Lukas Barth
Talla

Fafaroma yace kamata yayi mabiya darikar katolika su taimakawa dubun dubatar mutanen da ke neman mafaka, sakamakon barazanar yake yake da yunwa, don su sami su fara sabuwar rayuwa.
Shugaban na mabiyar darikar Katolika a duniya yace Annabi Isa Alaihis Salam ma haka ya taimaka wa mabukata a lokacinsa.
Wannan kiran na zuwa ne a daidai lokacin da wasu dubun dubatar bakin haure suka kara tsallakawa zuwa Jamus, inda kuma suka sami gagarumar tarba daga ‘yan kasar.
An ga jama’ar dake musu fatan alheri suna sowa tare da daga balam balam, a lokacin da ‘yan gudun hijiran suke saukowa daga jiragen kasa da suka kaisu kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.