Isa ga babban shafi
Faransa-Turai

Faransa na karbas taro kan halin da kananan kabilu ke ciki a gabar ta tsakiya

Yau Talata a birnin Paris na kasar Faransa, ana gudanar da taron kasa da kasa domin tattauna matsalolin da wasu kabilu da kuma mabiya tsirarrun addinai ke fuskanta daga mayakan ISIS, a kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.

Shugaban Faransa, François Hollande.
Shugaban Faransa, François Hollande. REUTERS/Charles Platiau
Talla

Kasashen Faransa da Jordan ne suka bukaci a gudanar da taron, wanda ke samun halarta wakilai daga kasashen duniya fiye da sittin da wasu kungiyoyi masu zaman kansu, lura da yadda mayakan da ke ikirarin jihadi ke ci gaba da yi wa tsirarun kabilu da kuma mabiya wasu addinai ke fuskantar barazana, musamman a kasashen Syria da Iraki.

Ko baya ga matakai na kariya da taron ke neman samar wa irin wadannan mutane a cikin kasashensu, akwai kuma batun yadda za a bai wa wadanda suka tsere daga yankin damar komawa gida a sawwake, amma tare da sa idon kasashen duniya.

Lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ranar 27 ga watan Maris da ya gabata, ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius, ya ce alhaki ya rataya a wuyan kasashen duniya, domin tabbatar da tsaro ga mutanen da ke fuskantar kisa da ta’annanti daga kungiyar ta ISIS a kasashen Gabas ta Tsakiya saboda dalilai na addini ko kuma kabilanci.

To sai dai taron wanda shugaba Francois Hollande ke jagorantar bikin budewa, ya zo ne a cikin wani yanayi da kasashen Turai ke fuskantar wata babbar barazana ta kwararar baki, sakamakon yake-yaken da ake fama da su a kasashen Larabawa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.