Isa ga babban shafi
TARAYYAR TURAI-BAKIN-HAURE

Kasashen Turai za su gana kan matsalar baki

Yau Kasashen Poland da Jamhuriyar Czech da Slovakia da kuma Hungary za su gudanar da wani taro a Luxembourg dake shugabancin kungiyar kasashen Turai dan tattauna matsalar bakin dake kwarara nahiyar wadda ke cigaba da ci musu tuwo a kwarya.

'Yan gudun hijirar na cikin wani mawuyacin hali a Turai.
'Yan gudun hijirar na cikin wani mawuyacin hali a Turai. REUTERS/Srdjan Zivulovic
Talla

Ministan harkokin wajen Poland Schetyna ya ce taron zai duba matakan gaggawa da kuma na dogon lokaci da za’a dauka dan shawo kan matsalar.

Ministan ya kara da cewa kowacce kasa tana da hurumin bayyana adadin bakin da zata iya dauka sabanin yadda ake tilasta mata.

An dai bayyana matsalar kwararar ‘Yan gudun hijirar na wannan lokaci a Turai a matsayin mafi kamari tun bayan yakin duniya na biyu yayin da wasu kasashen su ka bayyana aniyarsu ta karban wani kaso daga cikin 'Yan gudun hijirar, inda kuma wasu suka ki amince da hakan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.