Isa ga babban shafi
Austria

An yi Zanga-Zangan Nuna Goyon Bayan 'Yan Gudun hijira a Austria

Dubban jama’a suka yi zanga-zangan lumana yau a Vienna na kasar Austriya domin nuna goyon bayan su ga dimbin ‘yan gudun hijira daga Syria dake tserewa yakin kasar su zuwa Turai.

Wasu 'yan gudun hijira da suka sami shiga Austria
Wasu 'yan gudun hijira da suka sami shiga Austria rfi
Talla

Kasar Austriya na daga cikin wuraren da ‘yan gudun hijiran ke bi zuwa kasashen Turai, kuma kamar yadda masu jerin gwanon ke cewa mutane akalla 60,000 suka shiga zanga-zangan lumanan.

Mai Magana da yawun wadan da suka shirya zanga-zangan ya ce abin bukata shine a bar dukkan ‘yan gudun hijira su shiga inda suke bukata ba tare da gindaya masu wasu sharudda ba.

Dubban 'yan kasar Austriya na ta taimakawa 'yan gudun hijiran wajen basu wasu muhimman bukatu da suke bukata.

A watan jiya 'yan gudun hijira 170,000 suka shiga kasar Austriya, yawanci sun zarce zuwa Jamus da ma gaba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.