Isa ga babban shafi
Bakin-haure

bakin hauren nahiyar Afrika kusan 200 aka ceto daga hallaka a tekun kasar Spain

Bakin haure kusan 200 daga arewacin Afrika, aka kubutar daga salwanta a teku, a lokacin da suke kokarin kai gaban ruwan kasar Spain a kan hanyar su ta zuwa Turai.

Tawagar bakin haure zuwa turai ta Teku
Tawagar bakin haure zuwa turai ta Teku REUTERS/Italian Navy/Handout via Reuters
Talla

Mai Magana da yawun jamian kai daukin gaggawa na kasar Spain ya bayyana cewa bakin hauren 188 aka ceto daga cikin kwale-kwale.

Wani jamiin agaji na Red Cross ya shaidawa kamfanin Dillancin labaran Faransa AFP cewa, akwai ‘yan kasar Algeria 103 cikin bakin hauren, rabi kuma kananan yara ne.

A cewar wata hukuma dake sa idanu, kan bakin haure ta kasa da kasa, daga watan Janairun wannan shekara zuwa karshen watan tara, na shekarar da ta gabata, bakin haure 2, 819 suka bi ta mashin ruwan mai cike da hatsari daga gabar Arewacin nahiyar Africa zuwa kasar ta Spain akan hanyarsu ta zuwa Turai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.