Isa ga babban shafi
Faransa

An kame masu safarar wiwi a Faransa

Jami’an fasa kwabri a kasar Faransa sun yi nasarar kama wasu motoci da ke dauke da ton 7 na tabar wiwi a birnin Paris.

Jami’an fasa kwabri  a kasar Faransa sun yi nasarar kama wasu motoci da ke dauke da ton 7 na tabar wiwi
Jami’an fasa kwabri a kasar Faransa sun yi nasarar kama wasu motoci da ke dauke da ton 7 na tabar wiwi REUTERS/Jacky Naegelen
Talla

Shugaban Faransa Francois Hollande ne ya sanar da nasarar da jami’an suka samu bayan sun kwashe makwanni suna gudanar da bincike.

Hollande ya ce an samu tabar wiwin ne jibge a cikin wasu motocin da aka aje buhu buhu da nauyinsu ya kai sama da tone 7, kuma kudin su ya kai euro miliyan 15.

Ministan kudi Michel Sapin wanda ya ce wannan shi ne kamu mafi girma da aka taba yi a Faransa, ya sa shugaban kasar Francois Hollande ya ziyarci inda aka kama tabar, tare da jinjinawa jami’an tsaron da suka yi nasarar kame tabar.

Hollande ya ce nasarar wata babbar koma baya ne ga ayyukan kungiyoyin da ke safarar miyagun kwayoyi da kuma hada kai da Yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.