Isa ga babban shafi
Faransa

Za a yi zaman makoki na kwanaki uku a Faransa

Gwamnatin Faransa ta kebe kwanaki uku na zaman makoki daga ranar Litinin domin juyayin mutuwar mutane kusan 130 da aka kashe a munanan hare haren da ‘Yan ta’adda suka kaddamar a birnin Paris a daren Juma’a. sama da mutane 250 suka samu rauni a hare haren da aka kai a wurare da dama wanda aka bayyana mafi muni a Nahiyar Turai tun harin Madrid da aka kai a 2004.

An kai munanan hare hare a birnin Paris inda aka kashe mutane kusan 130
An kai munanan hare hare a birnin Paris inda aka kashe mutane kusan 130 REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

A ranar litinin al’ummar kasar za su yi natsuwar minti guda da rana misalin karfe 11 tare da sassauta tutar kasar.

An kai jerin hare haren ne da yammacin Juma’a a wuraren cashewa da cin abinci da filin wasan kwallon kafa.

REUTERS

Rahotanni sun ce kimanin mutane 300 ke kwance a gadon asibiti cikin mawuyacin hali.

Kungiyar IS da ke da’awar Jihadi a Syria ta yi ikirarin daukar alhakin kai jerin hare haren na kunar bakin wake da na ‘yan bindiga a birinin na Paris.

Maharan dauke da bindiga kirar AK47 sun abka wani gidan cashewa a Bataclan gabashin birnin Paris inda suka bindige mutane 82 tare da yin garkuwa da wasu.

Wasu da suka tsira sun ce maharan sun abka gidan cashewar suna yin kabbara, kuma an ji suna ambatar sunan shugaban kasar Faransa François Hollande suna cewa lafinsa ne, shi ya sanya suka kai harin saboda shiga tsakanin rikicin kasar Syria.

A lokaci guda kuma aka kai harin kunar bakin wake a kusa da filin wasan kwallon kafa a lokacin da Faransa ke buga wasan sada zumunci da Jamus da yammacin Juma’a.

A lokacin da ya ke jawabi akan harin na Paris, Shugaba Hollande yace wannan tamkar kaddamar da yaki ne akan Faransa Tare da daura alhakin harin akan Mayakan IS.

Faransa dai ta kaddamar da dokar ta baci- a lokacin hare haren tare da tsaurara matakan tsaro a sassan kasar da ofisoshin jekadancinta a kasashen duniya.

Hare hare dai sun girgiza duniya, inda shugabannin duniya ke ci gaba da aika wa Faransa da sakon yin allawadai da hare haren na Paris.

REUTERS/Christian Hartmann

Adadin wadanda suka mutu ba su kunshi maharan ba guda 8, kuma zuwa Assabar babu wanda ‘Yan sanda suka kama yayin da suke ci gaba da binciken hutunan na’urar kamara domin tantance gawarwakin maharan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.