Hollande ya bukaci kafa dokar ta baci watanni 3 a Paris
Shugaban kasar Faransa Farncois Hollande ya bukaci aiwatar da dokar ta baci na watanni uku a birnin Paris, wanda ake ganin zai kunshi ranakun gudanar da taron sauyin yanayi da za’a fara a karshen wannan watan.
Wallafawa ranar:
Majiya daga Majalisar kasar dake shaidawa Kamfanin dilancin Labaran faransa AFP batun, na cewa sanya wannan doka sama da kwannaki 12 na bukatar amincewar Majalisar kasar.
A yanzu dai alkallumar mamata harin Paris ya karu zuwa 132, bayan mutuwar wasu mutane 3 a yau lahadi cikin mutane sama da 350 da ke kwance a asibiti, yayin da wasu 42 yanzu haka ke cikin hali mai tsananin.
A ranar 30 ga watan Nuwamba ake saran fara taron sauyin yanayi da shugabanni duniya da dama za su hallatar a Birnin na Paris.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu