Mutumin da ya kitsa harin Faransa na zaune a cikin kasar
Hukumomin kasar Faransa sun ce su na kyautata zaton cewar mutumin da ya kitsa kazamin harin da aka kai Paris Abdelhamid Abaaoud yana nan a cikin kasar bai fice ba.
Wallafawa ranar:
Babban mai gabatar da kara a kasar, Francois Mollins ya ce, jami’an tsaro sun hallaka mutane biyu a samamen da suka kai a yankin St-Denis a jiya da asuba bayan harba harsasai sama da 5,000, yayin da suka kama wasu mutane 8 da ake yi wa tambayoyi yanzu haka.
Yau ake saran majalisar kasar za ta fara mahawara kan bukatar shugaba Francois Hollande na kara wa’adin dokar ta baci da kuma fadada dokar yaki da ta’adanci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu