Isa ga babban shafi
Rasha

Za a tsawaitawa Rasha takunkumin kariyar tattalin arziki

Mambobin kungiyar Tarayyar Turai sun amince su tsawaita wa kasar Rasha takunkumin kariyar tattalin arziki na tsawo wasu watanni 6, saboda zargin kasar da ruwa da tsaki a Ukraine.

Vladmir Putin Shugaban kasar Rasha
Vladmir Putin Shugaban kasar Rasha REUTERS/Sergei Karpukhin
Talla

Wata majiya daga kungiyar Turai tace zuwa ranar Talata ne kungiyar kasashen zata sanar da matakin na tsawwalawa Rasha Takunkumi na tsawon watanni 6.

Wannnan kuma na zuwa ne a yayin da kasashen na Turai ke neman hadin kan Rasha don kawo karshen rikicin kasar Syria.

Hukumomin Ukraine da kasashen Turai dai na zargin Rasha da kokarin mamaye yankunan Ukraine bayan ballewar yankin Crimea a watan Maris din 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.