Isa ga babban shafi
France

Faransa ta sami Mace ta farko da ta kamu da cutar Zika ta jima'a

Ministan Lafiya na kasar Faransa Uwargida Marisol Touraine ta sanar da samun mutun na farko a kasar daya kamu da mummunar cutar nan da ake kira Zika .

Ministan lafiya na Faransa Marisol Touraine.
Ministan lafiya na Faransa Marisol Touraine. REUTERS/Charles Platiau
Talla

A cewar Ministan wata mace ce wadda ta shigo Faransa daga Brazil aka auna ta aka ga cewa ta kamu da wannan cuta.

Bayanan na cewa an auna ta kwanakin da suka gabata, kuma mace ba ta da ciki.
Ministan ta shaidawa kamfanin Dillancin labarai na Faransa AFP.

Wannan cuta ta Zika na ta bazuwa a sassan duniya musamman a kudancin Amurka.

Masana na cewa ana kamuwa da wannan cuta ce sakamakon cizon sauro da kan sa mata masu juna biyu su haifi jinjiri da wata irin halitta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.