Isa ga babban shafi
Turai

Ana kashe kudi kan Tabar Wiwi a Turai

Wani Bincike ya nuna cewar ‘yan kasashen Turai na kashe euro biliyan 24 duk shekara wajen sayen kwayoyin da aka haramta amfani da su, da suka hada da tabar wiwi da hodar ibilis.

Ganyen Tabar wiwi
Ganyen Tabar wiwi AFP PHOTO / Juan Mabromata
Talla

Rahotan binciken ya bayyana fargabar cinikin da ayyukan ta’addanci.

Kungiyar da ke sa ido a kasashen Turai ce ta fitar da rahoton, sannan ya nuna cewar tabar wiwi da ake ciniki, ana noma ne a kasashen Turai, sai kuma hodar ibilis da ake shiga da shi Yankin, duk da ya ke yanzu haka an fara nomawa a wasu kasashen da ke cikin kungiyar.

Alexis Goosdeel, shugaban kungiyar da ke sa ido kan sha da safarar kwayoyi a kasashen Turai, yace ana samun riba sosai a cinikin haramtattun kwayoyin wanda ke barazana ga yankin.

Daraktan ‘Yan Sandan Turai, Rob Wainwright, yace kashi daya bisa uku na masu aikata laifufuka a kasashen Turai na mu’amala da haramtatun kwayoyin.

Jami’in ya kara da cewar, kashi 20 na masu safarar baki zuwa Turai na amfani da tabar wiwi ko kuma hodar ibilis.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.