Isa ga babban shafi
Spain

Rajoy zai kafa gwamnati a Spain

Firaministan kasar Spain Mariano Rajoy ya ce, abu ne mai yiyuwa ya kafa sabuwar gwmanati bayan da jam’iyyarsa ta masu ra’ayin rikau ta samu karin kujeru a zaben majalisar dokokin kasar da aka gudanar a jiya lahadi.

Firaministan Spain, Mariano Rajoy
Firaministan Spain, Mariano Rajoy REUTERS/Jon Nazca
Talla

Sakamakon farko na wannan zaben na nuni da cewa jam’iyyar, ta yi nasarar lashe kujeru 137 daga cikin 350 da ake da su a majalisar kasar, abin da ke nufin cewa ta samu karin kujeru 14 idan aka kwatanta da wadanda ta samu a zaben da aka gudanar cikin Disambar bara.

Ita kuwa jam’iyyar ‘yan gurguzu ta tashi da kujeru 85 wanda shi ne koma-baya mafi muni da ta taba fuskanta a tarihin siyasar kasar na baya-bayan nan.

Jam’iyyar masu tsatsauran ra’ayi ta Podemos kuwa wanda aka yi hasashen cewa za ta iya lashe zaben na jiya, ta tashi ne da kujeru 71.

Zaben wanda aka gudanar kwanaki kadan bayan da al’ummar Birtaniya suka yanke shawarar ficewa daga kungiyar Turai, ana kyautata zaton zai kawo karshen takaddamar siyasar da kasar ta Spain ta fada tun cikin watan Disambar da ya gabata, inda bayan kammala zabe aka kasa cimma jituwa a tsakanin jam’iyyun siyasa domin kafa sabuwar gwmanati.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.