Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta tsawaita dokar ta baci

Majalisar dokokin Faransa ta fara mahawara a wannan talata domin tsawaita wa’adin aiki da dokar ta baci da aka kafa a kasar, lura da yadda ayyukan ta’addanci ke ci gaba da addabar kasar.

Shugaba Francois Hollande ya gabatar da bukatar tsawaita dokar ta bacci a gaban Majalisar kasar
Shugaba Francois Hollande ya gabatar da bukatar tsawaita dokar ta bacci a gaban Majalisar kasar REUTERS/Michel Euler/Pool
Talla

Da farko dai gwamnati ta bayyana aniyarta ta kawo karshen aiki da dokar, to amma sakamakon harin da aka kai a birnin Nice wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 84, shugaba Francois Hollande ya ce yana son tsawaita dokar da akalla watanni shida nan gaba.

A cikin watanni 18 an kai munannan hare haren ta’addanci uku a Faransa wanda kuma ya yi sanadiyar mutuwar mutane 250.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.