wani matashi ne dan kasar Iran ya kai harin Munich na kasar Jamus
Akalla mutane 9 ne suka rasa rayukansu bayan wani dan bindiga ya kai hari a wani katafaren shagon siyar kayayyakin masarufi da ke birin Munich na kasar Jamus.
Wallafawa ranar:
Jami’an ‘yan sandan Jamus sun bayyana cewa, wani matashi ne dan kasar jamus dan asalin kasar Iran mai shekaru 18 a duniya ne, ya kai harin na jiya jumma’a.
Jaridar Bild ta Jamus ta rawaito cewa, an hangi maharin na bude wuta ba tare da kakkautawa ba a cikin katafaren shagaon saida kayyakin masarufin da ke kusa da wani filin wasannin Olympics kafin daga bisani ya ruga ta hanyar wata tashar jirgin kasa.
Tun lokacin da wani matashi dan kasar Afhanistan ya kai harin wuka kan fasinjojin wani jirgin kasa a Bavaria a ranar Litinin da ta gabata, jami’an tsaron Jamus ke cikin shirin ko-ta-kwana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu