Isa ga babban shafi
EU-Girka

Tarayyar Turai ta karawa Girka Euro Miliyan 115 saboda 'yan gudun hiujira

Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da bada kudin Turai Euro Miliyan 115 kari domin taimakawa ‘yan gudun hijira dake yankin kasar Girka, kwana daya bayan rahotanni da aka baza gameda mawuyacin halin da ‘yan gudun hijiran ke ciki.

'Yan gudun hijiya cikin layi don karban abinci a yankin kasar Girka
'Yan gudun hijiya cikin layi don karban abinci a yankin kasar Girka 路透社
Talla

Mai magana da yawun Hukumar Christos Stylianides ya ce Karin wadannan kudade za'ayi amfani da su ne wajen inganta rayuwan ‘yan gudun hijiran a sansanonin su, ciki akwai batun sama masu makarantu da taimakawa kananan yara.

A juma'a data gabata Hukumar Kare ‘Yancin Bil’adama ta fitar da wani rahoto dake nuni da halin kunci da ‘yan gudun hijira ke ciki a yankin Girka.

Samada mutane dubu 850 daga wuraren da ake tafka yaki a Syria, Iraki da Afghanistan ke samun a shekarar data gabata suka shiga Girka, bayan sun isa kasar cikin yanayi mai wahalarwa ta kananan kwake-kwale.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.