An zargi wata mata da hannu a yunkurin kai hari a Paris
Hukumomin tsaron kasar Faransa sun gurfanar da wata mata mai shekaru 29 gaban kotun sauraran kararraki kan ta’addanci a kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
An dai zargi matar mai suna Ornella G, da hannu a yunkurin kai harin ta’addanci a Birnin Paris kusa da ginin Cocin Notre Dame inda aka ajiye wasu tunkunyoyin gas guda 6.
Masu bincike sun ce sun gano hoton hannun matar a jikin mota kirar peejo da aka yasar nesa kadan da ginin cocin wadda ke dauke da tukunyoyin gas din da aka gano.
Hukumomin tsaron kasar Faransa sun kara tsaurara sa idanu kan mutane a kasar, a kokarinsu na dakile duk wata barazanar tsaro da ka iya tasowa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu