Isa ga babban shafi
Jamus-Faransa

Jami'an tsaro sun kame matasa uku a Jamus bisa zargin alaka da ta'addanci

Jami’an tsaro a kasar Jamus sun kame wasu matasa guda uku ‘yan Syria bisa zargin cewa Kungiyar ISIS ce ta tura su kasar, da nufin kai harin ta’addanci.

Jami'an tsaro a Jamus da ke gadin wata tashar jirgin kasa
Jami'an tsaro a Jamus da ke gadin wata tashar jirgin kasa 路透社
Talla

Ministan cikin gida na kasar Jamus, Thomas de Maizre ya shaidawa manema labarai cewa, suna zaton matasan na da alaka da wadanda suka kai hari a birnin Paris na Faransa, a watan Nuwamban shekarar da ta gabata.

Masu bincike sun ce sun gano cewa matasan, masu shekaru 17, 18 da kuma 26 sun shigo Jamus din ta hanyar bi ta cikin kasashen Turkiya da Girka tare da amfani da fasfunan bogi.

Jmai'an tsaro suna cigaba da bincika yiwuwa ko akasin haka na tabbatuwar alakarsu da kungiyar 'yan ta'adda.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.