Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa da Rasha da Jamus za su gana kan Ukraine

Shugabannin kasashen Faransa da Jamus da Rasha na shirin gudanar da wani taro a birnin Berlin don tattaunawa kan matakan magance rikicin gabashin Ukraine, in da kusan mutane dubu 10 suka rasa rayukansu.

Shugaban Faransa, Francois Hollande da takwaransa na Rasha Vladmir Putin
Shugaban Faransa, Francois Hollande da takwaransa na Rasha Vladmir Putin REUTERS/Alexander Zemlianichenko/Pool
Talla

Shugaba Francois Hollande na Faransa ya zanta da takwarorinsa na Rasha da Jamus ta wayar tarho dangane da shirya wannan taro da zai samu halartar shugaban Ukraine, Petro Poreshenko.

Sai dai wata sanarwa da fadar Hollande ta fitar, ta bayyana cewa, kawo yanzu ba a tsayar da ranar gudanar da taron ba, amma ana zaton za a yi shi ne nan bada jimawa ba.

Taron dai zai mayar da hankali ne kan warware ricikin gabashin Ukraine, in da mutane dubu 9 da 600 suka rasa rayukansu.

Gwamnatin Ukraine da kasashen Yamma sun zargi Rasha da rura wutar rikicin, amma Moscow ta musanta haka.

Wata yarjejeniyar zaman lafiya da Faransa da Jamus suka jagoranta a shekarar bara, ta taka rawa wajen sassauta rikicin amma ta gaza magance shi baki daya.

Faransa ta bayyana cewa, tsagaita musayar wuta ta din-din-din da kuma gaggauta karbe makamai na daga cikin sharuddan magance wannan riciki.

Faransa dai na kokarin shirya wannan taron ne a dai dai loakcin da ta ke samun sabani da Rasha, abin  da ma ya tirsasa wa shugaba Putin soke ganawa da Hollande a birnin Paris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.