Isa ga babban shafi
Faransa

Muhawara ta biyu a Jam'iyyar Republican ta Faransa

Wani binciken kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a Faransa, ya nuna cewa tsohon Firaministan kasar Francoise Fillon, ya zarta abokin takararsa Alain Juppe, wajen magoya baya, yayin da ya rage kwanaki a gudanar da zaben fidda gwani na Jam’iyyar adawa ta Republican zagaye na biyu.

Masu neman Jam'iyyar adawa ta Republican a Faransa ta tsayar da su a matsayin 'yan takararta na neman shugabancin Faransa François Fillon et Alain Juppé, yayin muhawarar da suka tabka.
Masu neman Jam'iyyar adawa ta Republican a Faransa ta tsayar da su a matsayin 'yan takararta na neman shugabancin Faransa François Fillon et Alain Juppé, yayin muhawarar da suka tabka. REUTERS/Eric Feferberg
Talla

Tsohon Firaministan Faransa Francois Fillon yace shi kadai ne zai iya kawo sauye sauye masu muhimmanci a kasar, a mahawarar da suka yi ta karshe kafin gudanar da zaben fidda gwani zagaye na biyu a karshen wannan mako.

Francois Fillon wanda ya bawa kowa mamaki wajen zuwa na farko a zaben fidda gwanin da akayi makon jiya, yace burinsa shi ne kawo kyakkyawan sauyi a kasar dake fuskantar barazanar bore.

Tsohon Firaministan yayi alkawarin rage ma’aikata 500,000 a cikin shekaru 5, da kuma soke sa’oi 35 na aikin da akeyi a cikin mako, domin farfado da tattalin arzikin kasar.

Fillon ya zargi abokin takarar sa Alain Juppe da cewar babu wani sauyin da zai iya kawowa a cikin kasar.

Ana shi jawabi, Alain Juppe yace rage yawan ma’aikata ba abu ne mai yiwuwa ba, duk da yake yana bukatar ganin anyi gagagarumin garambawul ba tare da bin hanyar da Fillon ke bukata ba.

Tuni dai tsohon shugaban kasar, Nicolas Sarkozy da ya zo na uku a zaben makon jiya, ya bayyana goyan bayan sa ga Francois Fillon.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.