Isa ga babban shafi
Faransa

Fillon ya zama dan takarar Republican a Faransa

Tsohon Firaministan Faransa Francois Fillon ya lashe zaben fidda gwanin takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar Republican bayan ya samu sama da kashi 65 na kuri’un da aka kada fiye da Alain Juppe.

François Fillon na jinjinawa magoya bayansa bayan samun nasara.
François Fillon na jinjinawa magoya bayansa bayan samun nasara. Reuters
Talla

Francois Fillon dai ya sami gagarumar nasara gaban Alain Juppe a zaben da aka gudanar a jiya lahadi zagaye na biyu.

Fillon ya kasance dan takarar da jam'iyyar Republican ta tsayar da ka iya zama shugaban kasar in har ya yi nasara akan abokan hammayarsa.

A jawabinsa na farko ga al'ummar kasar, Mista Fillon ya yi alkawarin inganta rayuwar jama'ar kasar ta hanyar sauya shugabancin Faransa.

Daga yanzu dai tsohon Firayi ministan kasar Nicolas Sarkozy ne zai kare martabar kalar tutar jam’iyyar ta Republican a zaben shugabancin kasar da za a gudanar a shekara mai zuwa.

Tuni dai Alain Juppé ya taya François Fillon murnar gagarumar nasarar da ya samu a zaben fitar da dan takarar shugabancin kasar na shekarar 2017.

Har ila yau bayan taya murnar da ya yi, Mr Juppe ya yi alkawarin bai wa  Fillon duk wata gudumowa da ta dace a zaben shugabancin kasar mai zuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.