Isa ga babban shafi
Faransa

Yau ake zaben fidda dan takarar jam'iyyar Republican

A yau lahadi al’ummar kasar Faransa ke zaben fidda gwani na dan takarar jam’iyyar Republican a zaben shugabancin kasar da za’a gudanar a shekara mai zuwa.

Yan takara karkashin jam'iyyar Republican Alain Juppe da Francois Fillon.
Yan takara karkashin jam'iyyar Republican Alain Juppe da Francois Fillon. JOEL SAGET / AFP
Talla

Tsofaffin firaiyi ministan kasar biyu da suka hada da Francois Fillon da Alain Juppe ne ke kokarin ganin sun sami nasara don tsayawa takara a zaben.

Fillon da Juppe sun sami nasara a zaben zagaye na farko da jam’iyyar Republican ta shirya.

Wanda ya lashe zaben ka iya kasancewa sabon shugaban kasar ta Faransa.

Tuni dai tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy ya fice daga yakin neman zaben shugaban kasar bayan munmunar kayen da ya sha a zaben fidda gwani da aka gudanar a makon jiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.