Isa ga babban shafi
Brazil

‘Yan majalisar Brazil sun bukaci rigar kariya daga tuhumar cin hanci

Shugaban Kasar Brazil Michel Temer ya sha alwashin hawan kujerar naki dangane da wata doka da yanzu haka Majalisar kasar ke shirin yi wadda za ta hana tuhumar su daga zargin cin hanci da rashawa.

Shugaban kasar Brazil Michel Temer
Shugaban kasar Brazil Michel Temer REUTERS/Carlo Allegri
Talla

Shugaban ya ce abu ne mai wuya ya amince da irin wannan doka, domin sun yi yarjejeniya a tsakanin su cewar babu dalilin yin haka.

Bincike ya bankado ‘yan majalisar kasar da dama da jam’iyyun siyasa sun karbi cin hanci daga kamfanin man kasar Petrobraz, kuma yanzu haka suna fargabar cewar ana iya daure su akai.

Matsalar cin hanci da rashawa ta haddasa matsaloli a shugabancin kasar Brazil, al’amarin da a baya ya kai ga tsige shugaba Dilma Roussef daga kujerar shugabancin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.