Isa ga babban shafi
Jamus

Merkel ta tsananta kan baki da musulmai a Jamus

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kaddamar da yakin neman zabenta da matakai masu tsauri kan bakin haure da haramta sanya hijabi ga mata Musulmi 

Uwargida Angela Merkel na fuskantar kalubale wajen neman wani sabon wa'adi a Jamus
Uwargida Angela Merkel na fuskantar kalubale wajen neman wani sabon wa'adi a Jamus REUTERS/Wolfgang Rattay
Talla

Uwargida Angela Merkel ta fuskanci matsaloli sosai kan matsayin da ta dauka na karbar baki, wanda hakan ya kai ga faduwar jam’iyyarta a zabubukan da a kayi.

Sai dai a wannan karon ta ce, ba za a sake samun matsalar ‘yan gudun hijirar da aka gani ba a kasar, in da kuma ta bayyana shirin haramta sanya hijabi ga mata Musulmi da kuma tabbatar da cewar bakin da ke zuwa kasar sun saje da ‘yan kasa.

Merkel da ke gabatar da sabon kudirin nata a taron jam’iyyarta ta CDU na shekara, ta samu goyon bayan wakilai kashi 89 cikin 100, wanda ke zama babban koma baya da take samu karo na biyu, bayan shekarar 2005 a matsayinta na shugarbar gwamnatin Jamus.

Shuagabar da ta shafe tsawon shekaru 11 tana jan ragamar mulkin kasar, a makon da ya gabata ta bayana aniyarta ta tsayawa takarar a karo na 4, wanda ake gani na tattare da babban kalubale a gare ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.