Faransa za ta tsawaita dokar ta baci saboda zabe
Gwamnatin Faransa ta sanar da shirinta na tsawaita dokar ta baci har zuwa bayan zaben da kasar za ta gudanar a shekara mai zuwa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Gwamnatin ta dauki matakin ne saboda karuwar barazanar hare-haren mayakan jihadi da kuma tabbatar da tsaro a lokacin gudanar da zaben.
A ranar Talata mai zuwa ne Majalisar Dokokin kasar za ta tafka muhawara kan tsawaita dokar, in da kuma Majalisar Dattawa za ta yi na ta zaman a ranar Alhamis don amince wa da matakin.
Faransa ta kafa dokar ce sakamakon harin da kungiyar IS ta kaddamar a birnin Parsi a bara, in da ta kashe mutane 130.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu