Isa ga babban shafi
Rasha

Fasinjoji 92 da ke Jirgin yakin Rasha sun salwanta a Teku

Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta ce jirgin yakinta mai dauke da fasinjoji 92 da ta sanar da bacewarsa, ya afka cikin tekun Bahar Maliya.

Jirgin yakin Rasha kirar Tu-154
Jirgin yakin Rasha kirar Tu-154
Talla

Rahotanni sun ce jirgin yakin ya bace ne bayan kimanin mintuna 20 da tashinsa daga yankin Sochi da ke kasar Rasha, da nufin zuwa birnin Latakia da ke Syria.

Wata tawagar jami’an ceto ce ta tabbatar da hadarin jirgin, bayan gano wasu daga cikin baraguzansa a gabar tekun da ke kusa da birnin na Sochi.

Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce jirgin yakin, kirar Tu-154 yana dauke ne da Jami’an kasar da suka kware wajen, kidan goge irin nasu daga sananniyar kungiyar da ta yi fice kan hakan wurin bukukuwa a kasar, mai suna ‘Alexandrov Ensemble, da kuma wasu ‘yan jaridu guda 9 sai kuma ma’aikatan jirgin guda 8, lokacin da jirgin yayi hadari.

Bainciken da jami’an Rasha suka gudanar ya nuna cewa ba rashin kyawun yanayi bane ya haifar da hadarin jirgin, lamarin da yasa suka zurfafa binciko dalilin faduwarsa.

Jirgin yakin dai hasali ya taso ne daga babban birnin kasar Moscow, inda ya sauka a fillin jiragen sama na Sochi tare da kara mai, inda ya kuma tashi zuwa birnin Latakia da ke Syria.

Har yanzu dai babu fasinja guda da rayu, da aka samu nasarar ganowa.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.