Isa ga babban shafi
Turkiya-Rasha

Rasha za ta binciki kisan jakadanta a Turkiya

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayyana kisan gillar da aka yi wa jakadan kasar a Turkiya Andrei Karlov a matsayin takala don yin zagon kasa ga sabuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Marigayi jakadan Rasha a Turkiya, Andrei Karlov gabanin bindige shi a bikin baje kolin hotuna
Marigayi jakadan Rasha a Turkiya, Andrei Karlov gabanin bindige shi a bikin baje kolin hotuna REUTERS/Ugur Kavas
Talla

Putin ya ce, amsar da zai bayar kawai ita ce, a ci gaba da yaki da ta’addanci, kuma lalle 'yan ta’adda za su dandana kudarsu.

Shugaban ya ce Rasha za ta tura da masu bincike zuwa birnin Ankara don gudanar da bincike kan kisan, bayan shugaba Recep Tayyip Erdogan ya amince da haka  a tattaunawar da suka yi  da Putin ta waya.
 

Shugaba Putin ta ce, dole ne ta gano wadanda ke da hannu a kisan jakadan wanda wani jami'in dan sanda ya bindige a wurin bikin baje kolin hotuna.

Bayan ya harbe shi har lahira, dan sandan ya bayyana cewa, wannan fansa ce akan rawar da Rasha ke takawa a rikicin kasar Syria, musamman a birnin Aleppo.

A bangare guda, Amurka ta rufe ofishin jakadancinta na Ankara bayan wani dan bindiga ya yi ta harbe-harbe a harabar ofishin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.