Isa ga babban shafi
Faransa

Farin jinin Fillon ya dushe a Faransa

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar adawa ta Republican a Faransa Francois Fillon, ya sha alwashin kare kanshi daga zargin ya azurta iyalin shi a lokacin da yana rike da mukamin Firaminista a majalisar kasar.

Dan takarar Republican François Fillon a zaben Faransa
Dan takarar Republican François Fillon a zaben Faransa REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Fillon na fuskantar matsin lamba daga wasu shugabannin jam’iyyarsa kan ya janye takararsa saboda yadda kuri’un jin ra’ayin jama’a ke nuna zai sha kaye a zaben shugaban kasa da za a gudanar a watan Afrilu.

François Fillon ya danganta zargin a matsayin yarfen siyasa, domin dagula yakin neman zabensa.

Sannan ya zargi gwamnatin gurguzu ta Hollande da kokarin yi ma shi zagon kasa, kamar yadda ya ke shaidawa ‘Yan majaliar jam’iyyarsa ta Republican a jiya a wata ganawar da ya yi da su a asirce.

A can baya dai Francois Fillon ne ake ganin zai lashe zaben shugaban kasar Faransa da za a gudanar watan Afrilu.

Amma sakamakon wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a kwana nan, ya nuna Fillon zai sha kaye tun a zagayen farko, saboda badakalar da aka bangado da ke zargin ya azurta matar shi da wasu ‘yayansa biyu ta hanyar karbar albashi a lokacin da yana rike da mukamin Firaminista.

Amma dan takarar ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyarsa su yi hakuri har sai bangaren shari’a ya kamala bincike akan matar shi da aka zarga ta karbi kudade da suka kai kimanin dubu dari tara na yuro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.