Isa ga babban shafi
Britaniya

Mazauna Britaniya na zanga-zangar ficewar kasar daga EU

Daruruwan 'yan kasashen Turai da ke zama a Birtaniya sun shiga wata zanga zangar da akayi a gaban Majalisar kasar a dai dai lokacin da take fara mahawara dan bai wa Firaminista Theresa May kaddamar da ficewa daga kungiyar Turai.

Mazauna Britaniya na zanga-zangar kin amince da ficewar kasar daga EU
Mazauna Britaniya na zanga-zangar kin amince da ficewar kasar daga EU REUTERS/Neil Hall
Talla

Masu zanga zangar dauke da tutocin kasashen da ke kungiyar Turai sun bukaci sanin makomar su idan Birtaniya ta kamala ficewa daga cikin kungiyar, yayin da wasu ke cewa a dakatar da ficewar.

Ana saran Majalisar ta kamala mahawara dan bai wa gwamnati damar kaddamar da ficewa daga kungiyar kamar yadda 'yan kasar suka amince.

A makon da ya gabata ne tsohon Friministan kasar, Tony Blair, ya bukaci 'yan kasar su jingine bukatar  ficewar kasar daga EU.

Mista Blair ya ce Barin EU da Britaniya ke shirin yi ba alheri ba ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.