Isa ga babban shafi
Venezuela

Venezuela: An yi zanga zanga ba tare da arrangama ba

Dubban masu zanga zanga a kasar Venezuela sun gudanar da tattaki a manyan biranen kasar cikin alhini mutane 20 da suka rasa rayukansu cikin makwanni 3 da suka shafe suna zanga zangar adawa da gwamnatin Nicolas Maduro.

Masu zanga zanga a kasar Venezuela
Masu zanga zanga a kasar Venezuela AFP/George Castellanos
Talla

Ba kamar yaddda aka saba gani ba, a wannan karon ba’a samu arrangama tsakanin jami’an ‘yan sanda da masu zanga zangar ba.

A karon farko tun bayan yamutsin da ya tashi a farkon watan Afrilu, masu zanga zangar sun ketara ta babban birnin kasar ta Venezuela, Caracas, da sauran yankunan kasar da ke marawa gwamnatin Maduro baya.

Jagoran ‘yan adawar kasar Henrique Caprilles ya bukaci al’ummar kasar da su koma zanga zangar gadan gadan a ranar Litinin mai zuwa, inda suka tsara tare manyan hanyoyi a kokarinsu na tursasawa shugaban kasar Nicolas Maduro sauka daga mukaminsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.