Isa ga babban shafi
Faransa

An zabi Macron shugaban Faransa

Hasashen karshe na sakamakon zaben shugaban Faransa zagaye na biyu da aka gudanar a yau Lahadi ya tabbatar da Emmanuel Macron a matsayin wanda ya yi nasara akan abokiyar hammayarsa Marine Le Pen.

Emmanuel Macron, tổng thống tân cử Cộng Hòa Pháp
Emmanuel Macron, tổng thống tân cử Cộng Hòa Pháp Ảnh FMM
Talla

Hasashen ya nuna Macron mai sassucin ra’ayi kuma mai da’awar Kungiyar Tarayyar Turai ya samu sama da kashi 65 na kuri’u yayin da Marine Le Pen mai tsattsauran ra’ayi ta samu kashi 34.9 na kuri’un da aka kada a zagaye na biyu.

Tuni dai hasashen kuri’un jin ra’ayin jama’a ke nuna Macron ne zai yi nasara a zaben da ya ja hankalin duniya.

Yanzu kalubalen da ke gaban Macron shi ne aiwatar da manufofinsa da suka hada da barazanar tsaro da rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa da inganta ilimi da sassauta dokokin kwadago.

Wannan ne karon farko a shekaru 60 da aka gudanar da zaben Faransa zagaye na biyu ba tare da ‘yan takarar manyan jam’iyyun siyasar kasar guda biyu ba.

Sakamakon zaben nada da  matukar tasiri ga makomar Tarayyar Turai, lura da girman Faransa a matsayin ta biyu ga karfin tattalin arzikin nahiyar da kuma karfin soji da fada aji a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

An fafata ne tsakanin ‘yan takara da manufofinsu suka yi hannun riga da juna, wato tsakanin mai da’awar Tarayyar Turai da kuma mai adawa da kungiyar.

A ranar 14 ga Mayu ake sa ran rantsar Emmanuel Macron a matsayin sabon shugaban Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.