Macron zai kawo cikas a ficewar Birtaniya- 'Yan adawa
Masu adawa da kungiyar kasashen Turai sun mayar da zazzafan martani game da zaben Emmanuel Macron a matsayin sabon shugaban Faransa, in da suka bayyana nasararsa da mummunan labari da ka iya haifar da cikas dangane da tattaunawar ficewar Birtaniya daga kungiyar kasashen Turai.
Wallafawa ranar:
A wannan Litinin, dan gani-kashenin ficewar Birtaniya daga kungiyar Turai Nigel Farage ya ce, shugaban hukumar kungiyar Turai Jean Claude Juncker, zai juya Emmanuel Macron yadda ya ke so a tattaunawar ficewar Birtaniya daga kungiyar.
Kungiyar da ke kyamar hadin kan kasashen Turai ta Birtaniya ta bayyana nasarar Macron mai shekarau 39 tamkar mika wuya ga ‘yan Nazi na Jamus.
Jaridar Telegraph da ake wallafawa a Birtaniya ta ce, akwai yiwuwar Mr. Macron ya ci gaba da aiki da zazzafan kudirin Faransa kan ficewar Birtaniya daga kasashen Turai.
Ita ma Jaridar Daily Mail wadda ta goyi bayan kada kuri’ar ficewar Birtaniya a bara, ta rawaito wani marubuci mai suna Robert Hardman da ke bayyana Macron a matsayin mai nuna banbbanci kan ficewar.
A lokacin yakin neman zabensa, Mr. Macron ya kyamaci kuri’ar da Birtaniya ta kada don raba dari da EU, yayin da ya bayyana hakan a matsayin babban laifi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu