Isa ga babban shafi
Faransa

Valls ya nuna sha’awar aiki tare da Macron

A Faransa, yanzu haka zababben shugaban kasar Emmanuel Macron da kuma mukarrabansa, na ci gaba da kintsawa domin samun rinjaye a zaben 'yan majalisar dokokin kasar da za a gudanar a watan gobe.

Tsohon Friministan Faransa a Jam'iyyar Socialist Manuel Valls da Sabon Shugaban kasa Emmanuel Macron.
Tsohon Friministan Faransa a Jam'iyyar Socialist Manuel Valls da Sabon Shugaban kasa Emmanuel Macron. REUTERS/Philippe Wojazer/File Photo
Talla

Daga cikin masu neman tsayawa jam'iyyar takara a zaben na 'yan majalisa har da tsohon Firaminista Manuel Valls, to sai dai ga alamar ya yi fargar jaji.

Zababben shugaban kasa Emmanuel Macron na fuskantar babban kalubale kafin sake hada kan 'yan kasar musamman a siyasance, lura da cewa da dama daga cikin wadanda suka mara masa baya a zaben da ya lashe sun fito ne daga jam'iyyun siyasa da ke da ra'ayoyi mabambanta.

A dai-dai lokaci da sabuwar jam'iyyar Macron ke kokarin tsayar da 'yan takara domin fafatawa a zaben 'yan majalisa da za a yi ranakun 11 da kuma 18 ga watan gobe ne, sai tsohon Firaministan kasar Manuel Valls, ya sanar da cewa yana son tsaya wa jam'iyyar takara a mazabarsa, to sai dai kwamitin riko na jam'iyyar ya ce Valls ya yi fargar jaji, domin tuni aka samu wanda zai tsayawa jami'iyyar a wannan yanki.

Valls, wanda ya rike mukamin firaminista tsakanin 2014 zuwa 2016, ya ce jam'iyyarsa ta asalin wato Socialist da ke kan karagar mulki a yau ta mutu, kuma yana fatan shiga a dama da shi a karkashin sabuwar gwamnatin Macron.

Kawo yanzu dai zababben shugaban kasar na ci gaba da nisanta kansa da jam'iyyar ta 'yan Socialist, kamar dai yadda yake cewa ba shi da alaka da jam'iyyar 'yan mazana jiya a kasar, sai dai nada sabon Firaminista da zai yi jim kadan bayan ranstar da shi a ranar lahadi mai zuwa ne watakila zai fayyace wa 'yan kasar irin mutanen da ya ke son yin aiki da su a gwamnatinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.