Edouard Philippe ya zama sabon Firayi ministan Faransa
Sabon shugaban kasar Fransa Emmanuel Macron ya nada Edouard Philippe dan majalisar dokoki, kuma magajin gari, da ya fito daga jam’iyar Republican a matsayin Firayi Ministansa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Masharhanta dai sun danganta sabon nadin da fatan da sabon shugaban kasar ke da shi na janwo bangarorin siyasar kasar 2, wato Republican da Socialiste wajen cimma burin manufofin da ya sa a gaba.
Macron yayi sabon nadin ne yayinda ya rage sauran wata guda a gudanar da zaben yan majalisar dokokin kasar, zaben da abokiyar hamayyarsa da ya kada Marine Le pen ta jam’iyyar National Front ta sha alwashin bai wa Macron mamaki.
Kafin wannan nadi dai za a iya cewa kusan tsawon makon da ya gabata sunan dan majalisar dokokin kuma magajin gari Le Havre daya daga cikin na hannun daman Alain Juppé, ya ci gaba da karakaina a kasar da fatan cewa wata kila ya dare kujerar ta Fira minista la’akari da cewa yana daga cikin wadanda ake ganin sun fi cancantar su rike mukamin, kamar yadda Benjamin Griveaux, kakakin jam’iyar Emmanuel Macron ya sanar.
Kusan dai abinda ya yi shugaba Macron, shine ya yi Edward domin shi ma ba wani sananne bane sosai a tsakankanin Faransawa, dan jam’iyar Republican ne a yanzu bayan da ya taba karbar katin jam’iyar socialiste shekaru 2 da suka gabata, lokacin da yake dalibi
Ya yi karatunsa na jami’a ne a fannin ilimin kimiyar siyasa, da kuma makarantar koyar da manyan ma’aikatan gwamnati.
Edouard Philippe ya yi aikinsa a matsayin mai zaman kai, kamar shugaban kasar.
PM da aka jima ana dakon nadin sa, na da nauyin kafa gwamnati a cikin kwanaki 2 masu zuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu