Isa ga babban shafi
Faransa

'Yan takara 7,882 na fafatawa a zaben 'yan majalisun Faransa

Ana cigaba da kada kuri’a a zagayen farko na zaben ‘yan majalisun kasar Faransa, wanda sshugaban kasar Emmanuel Macron ke fatan jam’iyyarsa ta Le Republic en Marche ta samu gagarumin rinjaye, wanda zai bashi damar aiwatar da manufofin gwamnatinsa a saukake.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron tare da matarsa Brigitte Trogneux a kan kekuna, yayinda al'ummar kasar ke dunguma zuwa rumfunan zabe don kada kuri'unsu a zagayen farko na zaben 'yan majalisar kasar.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron tare da matarsa Brigitte Trogneux a kan kekuna, yayinda al'ummar kasar ke dunguma zuwa rumfunan zabe don kada kuri'unsu a zagayen farko na zaben 'yan majalisar kasar. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Ana sa ran rufe rumfunan zabe da misalin karfe 4 agogon GMT a kananan garuruwan da ke kasar, yayinda sauran rumfunan zaben zasu cigaba da kasancewa a bude har zuwa misalin karfe 6 na yammaci agogon GMT, a sauran manyan biranen kasar ta Faransa.

Sakamakon kuri’ar wata jin ra’ayin jama’a da aka gudanar ta karshe kafin zaben ‘yan majalisun na yau, ya nuna cewa, jam’iyyar Macron zata lashe akalla kashi 30 na kuri’un da za’a kada a yau Lahadi, yayinda jam’iyyar Republican zata lashe kashi 20, sai kuma jam’iyyar National Front ta masu ra’ayin kishin kasa, da akai hasashen zata lashe kashi 17, na kuri’un da za’a kada a zaben na yau zagaye na farko.

‘Yan takara dubu bakwai da dari takwas, da tamanin da biyu ne zasu fafata neman a zabesu a tsakanin kujerun majalisar kasar ta Faransa 577 da ke akwai.

A yau Lahadi ne kuma Shugaba Macron zai gana da takwaransa na Cote d’Voire Alassane Ouattara, yayinda a gobe Litinin kuma zai gana da shugaban kasar Senegal Macky Sall duka a birnin Paris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.