Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

EU ta fara taro kan muhimman batutuwa a Brussels

An bude zaman taron kungiyar kasashen tarayyar turai EU, mai manbobi 27 hade da Birtaniya a birnin Brussels, wanda zai tattauna ficewar kasar ta Birtaniya daga kungiyar ta EU.

Fira Ministan Birtaniya Theresa May da Jakadan Birtaniya a kungiyar tarayyar turai EU Barrow, a birnin Brussels yayin da aka fara taron kasashen kungiyar 27 da kuma Birtaniya.
Fira Ministan Birtaniya Theresa May da Jakadan Birtaniya a kungiyar tarayyar turai EU Barrow, a birnin Brussels yayin da aka fara taron kasashen kungiyar 27 da kuma Birtaniya. REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Taron, shi ne na farko da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya halarta, wanda yake fatan ganin kasashen sun maida hankali, tare da sa ido, kan wasu kasashe da ke hada-hada a fannoni da dama da yankin na Turai, domin bin dokokkin da aka gindaya musu.

Kasashen da suka amsa goron gayyatar, zasu kuma tattauna kan batutuwa da suka shafi tsaro a nahiyar turan, da kuma shige da fice musamman na ‘yan cin rani a yankin na turai.

Masu bin lamuran siyasar nahiyar Turai, na kallon halartar Firaministan Birtaniya Theresa May, taron na Brussels, a matsayin zakaran gwajin dafi, tun bayan da kasar ta bukaci raba gari da kungiyar Turan.

Tsawon kwanuki uku shugabannin nahiyar turan, za su dukufa, domin bijiro da shawarwari, da za su taimakawa siyasar yankin, da nufin karfafa manufofinta ta fuskar tsaro, da kuma diflomasdiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.