Isa ga babban shafi
Birtaniya- EU

Firaministan Birtaniya Ta Kwantar Da Hankulan 'Yan Kasashen Waje Mazauna Birtaniya

Firaministan Birtaniya Theresa May ta sanar da cewa ‘yan asalin kasashen dake kungiyar Tarayyar Turai mazauna Birtaniya su kwantar da hankulansu game da dukkan fargaban matsayin su bayan ficewar Birtaniya daga kungiyar.

Firaministan Birtaniya  Theresa May
Firaministan Birtaniya Theresa May RFI
Talla

Uwargida Theresa May ta fito fili ta bayyana cewa ‘yan asalin kasashen Turai za’a bari su ci gaba da zama a Birtaniya ba tare da tsangwama ba,

Sai dai kuma shugaban jam'iyar adawa ta  Labour a majalisa  Jeremy Corbyn ta ce akwai abin dubawa cikin zancen.

Hankulan mazauna Birtaniya daga wasu kasashen da suka kai sama da miliyan uku, na tashe rashin sanin yadda za ta kasance masu tun bayan zaben raba gardama da aka gudanar a bara, don ganin Birtaniya ta fice daga cikin kungiyar kasashen mai wakilai 28.

Warware wannan batu dai na daga cikin batutuwa da aka fara tattaunawa akai tun makon jiya tsakanin Birtaniya da sauran kasashen Turai.

Firaminista Theresa May ta ce tana sane da cewa jama’a na fargaban yadda za ta kasance, amma kuma kada wannan ya zama abin fargaba.

A jawabinta mai shafuka 17  ta kuma bayyana jerin wasu bayanan da suka shafi sharudda game da iyali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.