Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

'Majalisar Amurka ta amince da sake kakabawa Rasha takunkumi

Shugabannin majalisar Amurka daga bangaren Republican da Democrats, sun amince da kudurin kakabawa kasar Rasha sabbin takunkumai, domin ladabtar da ita isa zargin sa hannu da ta yi a zaben shugabancin kasar na shekarar 2016.

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladmir Putin.
Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladmir Putin. newsoftheworld
Talla

Sabuwar dokar, ta kuma rage karfin ikon shugaban Amurka Donald Trump, na cirewa Rasha kowane irin takunkumi.

A gefe guda dai kundin tsarin mulkin kasar ya bai wa Trump, damar soke sabuwar dokar majalisar kasar, to sai dai duk wani yunkuri na daukar matakin, zai iya karfafa zargin da ake wa shugaban na alaka da Rashar, musamman kan taimaka masa wajen lashe zaben shugabancin kasar.

Matakin dai ya zo ne a dai dai lokacin da Trump ke yunkurin kyautata alaka diflomasiya da Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.