Isa ga babban shafi
Rasha- Amurka

Rasha ta gayyaci jami'an diflomasiyyar Amurka da ke Moscow

Ma’aikatar harkokin wajen Rasha, ta gayyaci wasu manyan jami’an diflomasiyar Amurka da ke Moscow, domin bada Karin bayani, kan shirin Gwamnatin Trump, na bada umarnin gudanar da binciken kwa-kwaf, a cibiyar lura da huldar kasuwancin kasa da kasa da diflomasiyya Mallakar Rashan da ke Washington.

Shugaban Rasha Vladmir Putin.
Shugaban Rasha Vladmir Putin. REUTERS/Alexander Zemlianichenko
Talla

A cewar Rasha gudanar da binciken ya sabawa ka’ida zalika mataki ne na tsokana da zai kara tsamin dagantaka tsakanin kasashen biyu.

Ana dai kallon matakin na Amurka a matsayin raddi ga umarnin da shugaban Rsha Vladmir Putin ya bada a watan Yuli da ya gabata, na maida jami’an diflomasiyyar Amurka da ke Moscow akalla dari 755 gida, a wani martani kan sabbin takunkuman da Amurka ta ayyana kan Rasha.

Tuni Rasha ta aike da wasikar korafi kan matakin na gwamnatin Amurka da ta ce ba zata lamunta ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.