Isa ga babban shafi
spain

Zaben raba gardamar 'yancin Catalonia a Spain ya gamu da tsaiko

Firaministan Spain Mariano Rajoy ya sanar da shirin daukan matakin shari'a domin hana zaben raba gardama don samun ‘yancin al’ummar Catalonia, inda yake cewa rashin biyayya ne kuma Spain ba za ta amince da shi ba.

Firaministan Spain Mariano Rajoy ke jawabi kan batun zaben raba gardamar 'yancin Catalonia da ake shirin gudanarwa, wanda ya ce ya saba doka.
Firaministan Spain Mariano Rajoy ke jawabi kan batun zaben raba gardamar 'yancin Catalonia da ake shirin gudanarwa, wanda ya ce ya saba doka. Reuters
Talla

Mariano Rajoy wanda ya kira taron gaggawa na kotun tsarin mulkin kasar domin gabatar da bukatar gayyatar kotun don fayyaci ra'ayinta dangane da zaben raba gardamar yankin Catalonia wanda za'a yi ranar 1 ga watan gobe, ya fadi cewa dukkan magadan garin 947 da ke yankin Catalonia an sanar da su cewa zaben raba gardamar kuskure ne.

Majalisar Yankin gunduman Catalonia, da ya hada da yankin Barcelona, tun Laraba da ta gabata suka jefa kuriar tsai da za su ci gaba da neman a yi zaben raba gardamar, al'amarin da ya farfado da rikicin siyasar da aka sani na kusan shekaru 40 da suka gabata.

A halinda ake ciki babban mai shigar da kara a Spain Jose Manuel Maza ya fadi cewa sun fara shirin gurfanar da Shugabannin Majalisar Catalonia da kuma jamian Gwamnati na yankin wadanda su ke shirin zaben raba gardamar domin za’a kwace takardun zaben raba gardaman.

Babban mai shigar da karan ya bayyana cewa sun sanar da ‘yan sanda domin su binciki batun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.