Isa ga babban shafi
Spain

Gwamnatin Spain ta kwace ikon lura da tsaron yankin Catalonia

Gwamnatin Spain ta dauki matakin maida ilahirin ayyukan ‘yan sandan yankin Catalonia karkashinta, domin hana gudanar da zaben raba gardamar da gwamnatin yankin ke kokarin gudanarwa, a ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa.

Fira ministan kasar Spain, Mariano Rajoy yayin taro da jiga-jigan jami'iyyarsa ta  (PP) a garin Palma de Mallorca, na kasar Spain, 23 ga Satumba, 2017.
Fira ministan kasar Spain, Mariano Rajoy yayin taro da jiga-jigan jami'iyyarsa ta (PP) a garin Palma de Mallorca, na kasar Spain, 23 ga Satumba, 2017. REUTERS/Enrique Calvo
Talla

A halin yanzu Diego Perez gwamnatin Spain ta nada a matsayin shugaban rundunar ‘yan sandan yankin na Catalonia., matakin da gwamnatin yankin ta ce ba zata amince da shi ba, domin kuwa karara hakan kutse ne bisa tafiyar da al’amuranta.

An dai sake tura dubban jami’an ‘yan sanda zuwa yankin, tun bayanda kotun kolin kasar ta Spain ta yanke hukuncin haramta kada kuri’ar raba gardamar, bisa neman ballaewar yankin na Catalonia.

Sai dai bisa dukkan alamu har yanzu shugabannin yankin na kan bakansu duk da kamen da dama daga cikinsu da ‘yan sandan Spain suka yi a makon da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.