IAEA ta yabawa Rasha na lalata makamanta masu guba
Hukumar da ke yaki da yaduwar makamai masu guba ta duniya, IAEA, ta yabawa Rasha saboda daukar matakin lalata makaman ta masu guba, inda ta bayyana shi a matsayin gagarumar ci gaba wajen raba duniya da makaman.
Wallafawa ranar:
Shugaban hukumar Ahmet Uzumcu ya kuma yabawa kasar wajen bai wa jami’an sa damar sanya ido domin lalata makaman wanda Rasha ta ce suna iya hallaka duk wani hallita da ke doran kasa.
Kasashen Rasha da Amurka sun mallaki tarin makamai masu guba wanda suka ce zasu lalata bayan sanya hannu kan yarjejeniyar kauda makaman a shekarar 2012.
Sai dai Rashan ta zargi Amurka da kin lalata nata makaman.
Rasha da ta gaji tarin wadannan makamai masu guba daga Tarayyar Soviet, Shugabanta Vladimir Putin ya ce matakin wani yunkurin ne na tabbatar da zaman lafiya a fadin duniya a cikin wannan karni.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu