Isa ga babban shafi
Spain

‘Yan Catalonia sun shirya wa zaben ballewa daga Spain

Shugabannin yankin Catalonia sun ce sun shirya wa zaben raba gardama domin ballewa daga Spain yayin da ya rage kwanaki biyu su jefa kuri’ar, duk da haramta zaben da mahukuntan Madrid suka yi.

Tutar yankin Catalonia da ke neman ballewa daga Spain
Tutar yankin Catalonia da ke neman ballewa daga Spain REUTERS/Juan Medina
Talla

A ranar Lahadi ne mutanen yankin na Catalonia ke fatar jefa kuri’ar a runfunan zabe sama da dubu biyu.

Kakakin Catalonia Jordi Turill ya shaidawa manema labarai cewa sun shirya runfunan zabe sama da dubu biyu da dari uku da jami’an zabe sama da dubu bakwai domin gudanar da zaben.

Mutanen Catalonia sama da miliyan biyar ke da ‘yancin jefa kuri’ar ta neman amincewa da ballewar yankin daga Spain.

Kotun kundin tsarin Spain dai ta haramta zaben, kuma mahukuntan kasar sun ba ‘yan sanda umurnin hana gudanar da zaben ta hanyar kwace kayayyakin zabe.

Sai dai har yanzu ‘yan sandan sun kasa gano inda aka boye akwatunan zaben.

An shafe kwanaki masu gabatar da kara na bada umurmin kame shugabannin shirya zaben raba gardamar.

Ko ya makomar Kungiyar Barcelona?

Masu sharhi kan sha’anin kwallo na diga ayar tambaya akan abin da zai kasance makomar kungiyar Barcelona.

Barcelona ta dade tana goyon bayan ballewar Catalonia, amma kuma ba ta son ficewa daga gasar La liga ta Spain.

Barcelona na son ci gaba da buga La liga idan yankin ya balle, kamar yadda Spain ta amince kungiyoyin Andorra kamar Cordoba su ci gaba da buga Lig din.

a wasan ranar Asabar da Barcelona za ta karbi bakuncin Las Palmas a Nou Camp, magoya bayan kungiyar sun bukaci ‘yan wasan su sanya Jasi kalar tutar yankin doruwa da Ja.

Amma shugabannin Barcelona sun yi watsi da bukatar inda kungiyar ta ce ‘yan wasan za su sanya jasinsu da suka saba Ja da bula.

Wasu kuri’un jin ra’ayin jama’a da aka gudanar sun nuna cewa ra’ayin mutanen Catalonia ya rabu biyu inda mafi yawanci suke son a yi zaben ta hanyar amincewar gwamnatin Spain.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.