Isa ga babban shafi
Faransa

Jami'an tsaron Faransa sun sa ido kan mutane 12,000

Ministan cikin gidan Faransa Gerard Collomb yace sabuwar dokar yaki da ta’addanci da ta fara aiki jiya Laraba, zata bada damar tsare wasu mutane 20 a gidajen su.

Wasu jami'an tsaron Faransa da ke cikin rundunar yaki da ta'addanci ta musamman, yayin da suka kai samame a yankin Saint Denis, da ke arewacin birnin Paris.
Wasu jami'an tsaron Faransa da ke cikin rundunar yaki da ta'addanci ta musamman, yayin da suka kai samame a yankin Saint Denis, da ke arewacin birnin Paris. REUTERS/Jacky Naegelen
Talla

Ministan ya kara da cewa yanzu haka jami’an tsaron kasar, na sanya ido kan mutane 12,000 domin kaucewa duk wata barazana.

Collomb yace za su yi iya bakin kokarin su wajen daukar matakan kare hakkin al’ummar kasar, yayin aiwatar da wannan doka.

A farkon makon da muke ciki ne shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya sanya hannu kan sabuwar dokar yaki da ta’addancin kasar wadda za ta bai wa hukumomi damar shiga gidajen jama’a domin gudanar da bincike, da kuma rufe wuraren ibada, sai kuma hana wadanda ake zargi da alaka da ta’addancin tafiye-tafiye.

Dokar ta bacin ta maye gurbin wadda aka kafa bayan harin da aka kai a birnin Paris cikin shekara ta 2015.

Sabuwar dokar, ta bai wa mahukuntan Faransa ‘yancin kula da tsaron wani babban taro ko wani wurin da ke fuskantar barazanar hari ba tare da neman izinin kotu ba.

Sannan dokar ta ba jami’an tsaro, ‘yancin gudanar da binciken kwa-kwaf ba tare da neman izinin wani ba.

Dokar ba bayar da izinin rufe duk wani wajen ibada na tsawon watanni shida da ke yada fatawar tsattsauran ra’ayi.

Sannan izinin mallakar bindiga ya koma hannun gwamnatin Tarayya.

Sai dai kungiyar Amnesty international ta koka kan yadda hukumomin tsaron Faransa ke amfani da dokar ta-baci, wajen hana al’umma gudanar da zanga zangar da dokar kasa ta basu dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.