Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta dakile hare-haren ta'addanci 12

Gwamnatin Faransa ta bayyana cewa, jami’an tsaron kasar sun yi nasarar dakile hare-haren ta’addanci har 12 da aka yi shirin kai wa kasar a cikin wannan shekarar.

Jami'an tsaron Faransa na cikin shirin ko ta kwana
Jami'an tsaron Faransa na cikin shirin ko ta kwana REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Ministan cikin gidan Faransa Gerard Collomb ne ya sanar da haka, in da kuma ya gargadi cewa, har yanzu akwai gagarumar barazanar hari da kasar ke fuskanta.

Minsitan ya ce, daga cikin hare-haren da aka dakile, har da wanda aka shirya kaddamarwa kan cibiyar horar da sojojin saman kasar da ke kudancin garin Salon de Provence.

Kazalika ‘yan ta’addan sun shirya kai farmaki kan barikokin soji da ofisoshin jami’an ‘yan sanda, sai kuma wasu manyan shaguna kamar yadda Mr. Collomb ya yi karin bayani.

Garkuwa da mutane bayan harin na daga cikin abubuwan da ‘yan ta’addan suka yi nufin aikatawa amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba, in ji Ministan cikin gidan.

'Yan Majalisun Faransa na nazari domin samar da dokar da za ta maye dokar ta bacin da aka kafa sakamakon harin da kungiyar ISIS ta kai wa kasar a shekarar 2015, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 130.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.