Isa ga babban shafi
Faransa

Netanyahu zai gana da Emmanuel Macron a Paris

Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu zai gana da Shugaban Faransa Emmanuel Macron a yau lahadi a fadar Elysee dake birnin Paris na kasar ta Faransa,Hukumomin Isra’ila da Faransa zasu tattaunawa ne kan batuttuwa da suka shafi rikicin gabas ta tsakiya, barrazanar kasar Iran kan Isra’ila.

Masallacin birnin Qudus a Isra'ila
Masallacin birnin Qudus a Isra'ila ©EUTERS/Ronen Zvulun
Talla

Zuwan firaministan Isra’ila a Faransa ya haifar da fushin faransawa dake goyan bayan batun zaman lafiya a yankin, sun gudanar da zanga-zanga don nuna bacin ran su ga matakin da Shugaban Amurka ya dau na ayyana birnin Qudus a matsayin babban birnin kasar Isra’ila.

Ana sa ran Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya shawo kan Benjamin Netanyahu don gani ya yi watsi da bukatar shugaban Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.