Isa ga babban shafi
Cataloniya

An kammala yakin neman zaben Catalonia

An kammala yakin neman zaben da ake shirin gudanarwa gobe alhamis a yankin Catalonia da ya yi yunkurin ballewa daga Spain, lamarin da ya kai ga cafke wasu shugabannin yankin yayin da wasu suka yi hijira.Samun galaba ko kuma akasin hakan, shi ne zai fayyace makomar ‘yan awaren yankin a zaben na gobe

Muhawarar yan takara a zaben Cataloniya
Muhawarar yan takara a zaben Cataloniya Capture d'écran
Talla

Ranar alhamis 21 ga wannan watan disemba ne al’umar yankin Cataloniya za su isa ruhunan zabe domin zaben wakilan Majalisar yankin.

Za a gudanar da zaben a yankin arewa maso gabacin Spain,yankin Cataloniya wanda zaben zai kasance zakaran gwajin dafi ga al’umar Cataloniya a yunkurin Shugaban yan aware na yankin dake gudun hijira a Bruxos Carles Pudgemont da wasu daga cikin mukaranban sa.

Baiwa yan aware rijaye zai nunawa duniya cewa mutanen yankin Cataloniya na goyon bayan kokarin tsohuwar Majalisar yankin a karkashin Carles Pudgemont , akasin haka zai nuna adawar mutanen Cataloniya da shirin neman balewar Cataloniya daga Spain.

A jajubirin rufe gangamin zaben yankin Cataloniya Carles Pudgemont ya kira wani babban taro a birnin Bruxos .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.