Isa ga babban shafi
Holland

Ministan Holland ya yi murabus saboda sharara karya

Sabon Ministan Harkokin Wajen Holland, Halbe Zijlstra ya sauka daga mukaminsa bayan sharara karya kan ganawar da ya ce ya yi da shugaban Rasha Vladimir Putin shekaru 12 da suka gabata.

Ministan Harkokin Wajen Holland mai murabus, Halbe Zijlstra a lokacin da ya fito daga Majalisar Dokokin Kasar bayan bayyana murabus dinsa
Ministan Harkokin Wajen Holland mai murabus, Halbe Zijlstra a lokacin da ya fito daga Majalisar Dokokin Kasar bayan bayyana murabus dinsa Martijn Beekman / ANP / AFP
Talla

Cikin hawaye ministan ya shaida wa Majalisar Dokokin Kasar cewar, ba shi da abin yi da ya wuce ya mika wa sarkin kasar takardar sauka daga mukaminsa.

Gabanin saukarsa, an shirya cewa, yau Laraba ne Ministan zai tafi birnin Moscow domin ganawa da takwaransa Sergei Lavrov game da kakkabo jirgin Malaysia a shekarar 2014.

Firaminista Mark Rutte ya bayyana abin da ya faru a matsayin babban kuskuren da ya taba yi a rayuwarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.